Gwamnan jihar Katsina minu Bello Masari ya buƙaci mazauna garuruwan da yan bindiga su ka addaba da su ɗauki makamai don kare ka su.

Aminu Masari ya bayyana haka ne yayin da ya je ziyarar ta’aziyya ga iyalan mutanen  da motar kwastam ta kashe su su goma.

Gwamna  ya bayyana haka ne a yau Talata wanda y ace mika wuya da mutanen ke yi ga ƴan bindigan ne ya sa su ke ci gaba da gudanar da ayyukan ta’adanci.

Gwamna Masari y ace harkar tsaro ba gwanati kaɗai ta shafa ba, ta shafi dukkan yan ƙasa kowa na da haƙki a kan tsaro.

Sannan gwamnan y ace kada su yadda da duk wani hasafi da hukumar kwastam za ta bas u har sai sun tabbatar an nema wa iyalan mutanen da aka kashe haƙƙin su.

A ƴan kwanakin nan ne motar kwatsam ta kashe wasu mutane goma a Katsina yayin da su ka biyo wata mota da ake zargi na ɗauke da shinkafa.

Al’ummar garin Jibia a Katsina na kokawa a kan yadda jami’an hukumar kwastam ke halaka musu yan uwa da sunan kama masu fasa kwauri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: