Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta buƙaci ƴan bindigan da su ka addabi jihar da su miƙa wuya ko kuma su fuskanci hukunci.

Hakan na ƙunshe a wani saƙo da sabon kwamishinan ƴan snadna jihar Yakubu Elkana ya fitar da nufin gargaɗi ga ƴan bindigan.

Sabon kwamishinan ya ce rununar ba za ta amucni ci gaba da ayyukan ƴan bindiga a jihar ba kuma za su ɗauki mataki a nan gaba.

Kwamishina Elkana y ace zai yi aiki da kwarewa don ganin an samu sauyi daga ayyukan yan bindiga wadanda su ka dade su na ta’addanci a jihar.

Sannan za su yi amfani da ƙarfin da kundin tsarin mulki y aba su don murƙushe su.

Kwamishinan ya sha alwashin daƙile duk wani aikin ta’addanci ko tayar da hankali wadanda su ka tsallake tsarin doka a jihar.

Tare da gargadi gay an bindigan da su ka addabi jihar da su ajiye makamansu tare da miƙa wuya ko kuma su fusknaci hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: