Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da buɗe makarantu saga ranar 23 ga watan daga muke ciki.

Gwamnatin ta bayar da umarnin bude makarantun sakandire kuma ƴan aji uku na ƙaramar sakandire abin ya shafa.

Hakan zai bayar da dama a gare su don ubuta jarrabawar da za ta bas u damar shiga babbar sakandire.

Hakan na ƙunshe a wata sanarwa da da kwamishinan ilimi a jihar Kaduna Dakta Muhammad Shehu Usman wadda yay i a ranar Laraaba.

Ya ce ɗaliban za su dinga zuwa makarantar ne da kayan gida.

Za a buɗe makarantun ne dga ranar 23 ga watan Agustan da muke ciki zuwa ranar shida ga watan Satumba.

Gwamnatin Kaduna ta rufe makarantun ne saboda shawarwarin da jami’an tsaro su ka bayar.

Ƴan bindiga sun addabi jihar Kaduna tare da sace ɗalibai wadanda har yanzu akwai da yawa daga cikin su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: