Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari garin Rini a ƙaramar Hukumar Bakura tare da sace mutane sama da 70.

Ƴan bindigan sun shiga garin ne a misalign ƙarfe biyu da rabi na dare.

Yayin da su ka shiga garin sun je Sabon Gari, Makarantar Boko, sannan su ka dangana zuwa babban garin Rini su ka kwashe mutanen.

Ƴan bindigan sun yi ta harbe-harbe da bindigun su lamarin da ya sa mutane su ka firgita tare da kasa fitowa waje.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da sace mutane kusan sittin a garin da ke ƙaramar hukumar Bakura.

Kakakin ƴan sandan jihar SP Muhammad Shehu ya tabbatar da hakan wanda ya ce an aike da kwararrun jami’an tsaro domin ceto mutanen da a ka sace.

Idan ba a manta ba a watan da mu ke ciki yan bindiga su ka shiga wata kwaleji a Bakura tare da sace ɗalibai har ma su ka nemi a bas u kuɗin fansa naira miliyan 350.

Leave a Reply

%d bloggers like this: