Rundunar ƴan sanda a Katsina ta kama wasu mutane wadanda su ke kai wa yan bindiga bayanan sirri don kai hare-hare ga jama’a.

Hakan ya fito daga bakin kakakin ƴan sandan jihar SP Gambo Isa wanda ya bayyana a yayin taron manema labarai ranar Juma’a.

Ya ce an kama mutanen ne a Ruwan Godiya da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Mutanen na amfani su ke bai wayan bindiga bayanai a kan abubuwan da ke faruwa a tare da yi wa jami’an tsaro kwanton ɓauna.

Waɗanda aka kama na haɗa kai da shugaban ƴan bindiga wanda ake kira Alhaji Ado Buji.

Sanarwar yan sandan ta ƙara da cewa akwai wani mai suna Malam Mustafa Isa wanda ya gabatar da Abdullahi Sani a wajen shugaban ƴan bindigan.

Kakakin yay i kira ga jama’a da su dinga sa ido domin akwai babban hatsari ga mutanen da ke cikin al’umma sun a bayar da bayanai ga ƴan bindiga.

An kama mutanen ne a ranar 12 ga watan Agustan da muke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: