Gwamnatin jihar Nassarawa ta ce mutane 800 a jihar sun kamu da cutar amai da gudawa.

Cutar amai da guawa ta shiga cikin ƙananan hukumomi 13 na jihar.

Darakta a hukumar lafiya ta jihar Dakta Ibrahim Alhassan ne ya bayyana wa jaridar Punch A Lafia.

Ya ce daga cikin mutane 800 da su ka kamu a cutar an salami wasu bayan sun warke daga cutar.

Dakta Ibrahim Alhassan ya ce mutane 800 da aka samu sun a ɗauke da cutar gaba daya an same su ne a shekarar da mu ke ciki.

Gwanatin jihar ta ce ta fara ɗaukar matakar wayar da kai a kan yadda mutane za su kare kan su daga kamuwa da cutar.

Gwamnatin Najeriya ta ce an samu ɓullatr cutar a jihohin ƙasar wanda ta halaka mutane da dama.

A wannan lokaci akwais abuwar cutar Korona nau’in Delta da ke cikin al’umma a halin yanzu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: