Rundunar sojin Najeriya ta bayyana nasarar kashe mayaƙan Boko Haram da dama a jihar Borno.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafin ta na Facebook.

Rundunar ta ce ta kashe mayaƙan ne a ƙauyen Ali Gambari.

Ta samu nasarar ne bayan bude wuta da ta yi a kan mayaƙan sannan ta yi nasarar kwato bindigu ciki har da bindiga ƙirar AK47 guda uku da alburusai masu tarin yawa.

Haka kuma rundunar ta samu wasu kwayoyi da wayar hannu da sauran wasu kayayyaki.

Babban hafsan sojin Najeriya Birgediya Janar Farouƙ Yahaya ya yabawa jami’an sa a bisa ƙoƙarin da su ka yi a kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: