Rundunar ƴan sanda jihar Legas ta gurfanar da wata mata mai shekaru 56 a duniya bisa zargin satar jariri sabuwar haihuwa.

Rundunar ta gurfanar da matar mai suna Bolanle Yomi gaban kotun majistire a jihar.
Ƴan snada sun gurfanar da matar bayan an samu bayanai da su ke nuni da cewar matar ta sace jaririn tare da kai shi wani wajen daban.

Matar ta sace jaririn ne yayin da babar sa ke bacci amma daga baya a ka gano ta sannan a ka kama ta.

Matar da ake zargi ta amsa lafin ta tun a wajen yan sanda sannan ta ce ba ta tafi da jaririn ne da nufin sace shi ba.
Alƙalin kotun Mista A.O. Layinka ya bayar da belin matar a kan kudi naira dubu ɗari.
Haka kuma ya bayar da umarnin ci gaba da tsare ta a gidan gyaran hali har sai ta cika sharudan belin da aka bayar a kan ta.
Sannan ya ayyana ranar 6 ga watan Oktoba a matsayiin ranar da za a ci gaba da shari’a a kai.