Gwamnan Borno Babagana Zulum ya ce sau hamsin ƴan Boko Haram su na kai masa hari.

Ya bayyana haka ne yau a Abuja.

Aƙalla mutane sama da dubu ɗari ne su ka rasa raukan su a sakamakon rikicin Boko Haram a jihar Borno.

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ne ya bayyana haka a yayin da yak e amsa tambayoyi daga ƴan jarida a yau Talata.

Gwamnan ya bayyana haka ne a Abuja bayan ya gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Ya ce a halin yanzu akwai mayaƙan Boko Haram 2,600 wadnada su ka tuba su ka ajiye makaman su.

Gwamna Zulum ya ƙara da cewa, akwai matasa masu yawa a cikin mayaƙan Boko Haram da su ka tuba sannan sun kware wajen sarrafa bindiga ƙirar AK47.

Haka kuma daga cikin wadanda su ka tuba akwai waɗanda a ka tilasta musu shiga ƙungiyar ba da son ran su ba.

Haka kuma shi kan sa mayaƙan Boko Haram sun kai masa hari kusan sau hamsin.

Sannan gwamnatin sa za ta tallafawa yaran da su ka rasa iyayen su a sanadin rikicin Boko Haram.

Gwamna  Zulum ya ziyarci shugaban ƙasa Buhari a fadar sa da ke Abuja don tattauna wa a kan mayaƙan Boko Haram da su ka tuba a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: