Gwamnatin jihar Taraba ta bayana cewar mutane bakwai sun mutu a garin sanadin wata cuta da ake zargin cutar amai da gudawa ce.

Kwamishinan lafiya a jihar Dakta Innocent Vakai ne ya bayyana haka jiya Litinin a Jalingo babban birnin jihar.
Ya ce mutanen sun mutu ne a garin Tella da ke ƙaramar hukumar Gassol ta jihar.

Tuni ma’aikatar lafiya haɗin gwiwa da kwararrun jami’an lafiya su ka isa garin don lalubo abin da ke faruwa.

A na zargin cutar amai da gudawa ce ta yi sanadiyyar rasa rayukan mutanen.
A cewar kwamishinan lafiya na jihar akwai wasu mutane 25 da aka kwanytar a asibiti kuma ake zargin sun a ɗauke da cutar amai da gudawa.
Hukumomi a jihar sun yi kira ga jama’a da su kasance masu tsaftace muhallin su don gudun ci gaba da yaduwar cutar a faɗin jihar.