Bayan kwanaki 88 da sace ɗaliban makaranatar Islamiyya ta Tegina a jihar Neja a yau ɗaliban sun shaki iskar ƴanci.

Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewar ɗaliban da a ka saki sun haura 70.

An sace ɗaliban ne sannan a ka nemi kuɗin fansa naira miliyan 150.

Iyayen ɗaliban sun shiga tara kuɗi domin fanso ƴaƴan su a baya.

Sai dai babu rahoton ko sai da a ka biya kuɗin kafin sakin ɗaliban a yau.

Jihar Neja na shan fama da hare-haren yan bindiga da ke halaka mutane a lokuta daban-daban.

Leave a Reply

%d bloggers like this: