Hukumomi a jihar Kogi sun bayyana cewar cutar amai da gudawa ta halaka mutane takwas a jihar.

Wani a ma’aikatar Lafiyar ta jihar ne ya bayyana haka wanda ake zargin sutar ta ɓulla a kananan hukumomi uku na jihar.

Baya ga kutane takwas da cutar ta halaka akwai wasu mutane sama da sittin waɗanda su ka kamu da cutar su ke kwance a asibiti.

Gwamnatin jihar ta fara bibiya a kan sanadin yaɗuwar cutar.

Ta ce mafi yawan mutanen da su kaa mutu sun mutu ne a gida kafin garzayawa da su asibiti.

Tuni a ka fara ɗaukar matakan wayar da kan jama’a yadda za su kare kan su daga cutar.

A na zargin cutar ta yaɗu ne sanadin amfani da abinci daa ruwan sha gurɓatacce.

Leave a Reply

%d bloggers like this: