Rundunar ƴan sanda a Katsina sun tabbatar da cewar ƴan bindiga sun kashe wasu mutane bakwai a wani hari da su ka kai ƙaramar hukumar Ƙanƙara ta jihar.

Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari garin Ɗan-Kumel a ƙaramar hukumar ƙanƙara tare da kashe mutane 11.
Maharan sun kai hari ƙauyuka 11 na garin a daren Alhamis wayewar Juma’a.

Wani mazaunin garin daga cikin ƙauyukan da a ka kai harin ya shaida cewar da shigar su su ka fara harbi kan mai uwa da wabi.

Sannan an samu wasu daga cikin mutanen garin wadana su ka samu munanan rauni kuma tuni a ka kais u asibiti don kula da lafiyar su.
A kwanakin baya kada gwamnan jihar ya bai wa ƴan jihar umarnin daukar makami domin su kare kan su.
Al’amarin da gwamnatin tarayyar Najeriya ba ta aminta da shi ba tare da ƙin goyon bayan hakan.