Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ƴan bindiga sun halaka mutane uku a ƙaramar hukumar Zangon Kataf.

Kwamishinan al’amuran tsaro a jihar Samuel Aruwan ne ya sanar da haka ya na mai cewa ƴan bindigan sun kai hare-haren ne  a kai a kai.

Hare-haren da ƴan bindigan su ka kai ranar Juma’a a ƙauyukan Manuka da Machun.

Ƴan bindigan sun shiga garin ne sannan su ka fara harbin mutane.

Baya ga mutane uku da aka halaka akwai mutane masu yawa da a ka raunata.

Samuel Aruwan ya ce jami’an tsaro sun isa garin kuma sun jiyo ƙarar harbe-harben da ƴan bindiga su key i a garin.

A wani labarin kuma ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Zangon Shanu a Zaria ta jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a daren Alhamis wayewar Juma’a sannan su ka yi garkuwa da mutane shida.

Wani mazaunin garin ya shaida cewar ƴan bindigan sun shiga ƙauyen ne da mislin ƙarfe ɗaya na dare, sannan su ka tafi da mutane shida kuma har yanzu ba a kai ga gano inda a ka tafi da su ba.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: