Gwamnatin jihar Zamfara ta samar da wasu dokoki a wanis alo na rage ayyukan ƴan bindigan da su ka addabi jihar.

Gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle ne ya bayar da umarnin rufe dukkanin kasuwannin jihar waɗanda su ke ci mako-mako.

Haka kuma gwamnatin ta haramta siyar da fetur  a gefen titi tare da haramta zuba shi a cikin galan.

Daga cikin matakan gwamnatin ta taƙaita safarar kayan abinci tare da tabbatar da bayar da cikakken bayani a kan abincin da kuma inda za a kai.

Gwamnatin ta haramta wa gidajen mai  da su ke ƙauyuka siyar da mai sai a cirnin gudau da helkwatar ƙananan hukumomi.

Sannan gwamnatin ta haramta shige da ficen kayan abinci daga Zamfara Illa waɗanda za a yi a cikin jihar kaɗai.

Dukkanain  waɗannan matakai an samar da su ne don daƙile ayyukna ƴan bindiga da su ka ƙi ci su ka ƙi cinye wa a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: