Gwamnattin jihar Plateau ta sassauta dokar hana fita wadda ta saka a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.

Hakan ya fito daga bakin gwamnan jihar wanda ya yi jawabi a yau Litinin.
Ya ce an sassauta dokar ne daga ƙarfe shida na safe zuwa ƙarfe shida na yamma.

Gwamnan jihar Simon Lalong ya ɗauki matakin hakan ne bayan shawarwaroi daga jami’an tsaro a kan rikicin da ya auku a jihar.

A sanarwar da yay i, gwamna Lalong y ace an kama wadanda su ka kitsa kai hare-hare a jihar kuma za a gurfanar da su a gaban kotu.
Haka kuma an sassauta dokar hana fita a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu da kuma Bassa daga ƙarfe shida na safe zuwa ƙarfe goma na dare.
Sannan dokar hana talla da tuƙa babur mai ƙafa uku wanda a ka fi sani da adaidaita sahu za ta ci gaba da zama kamar yadda a ka saka ta a kwaryar birnin jihar.
Rikicin Jos a kwananan ne ya fara ne yayin da wasu mabiya addinin kirista su ka yi wa musulmi matafiya kisan gilla.
Ko a makon da ya gabata sai da wasu su ka ƙona mallatai biyu tare da shaguna 14 a ƙaramar hukumar Jos ta kudu.