Gwamnatin jihar Kano ta ƙara kwanakin hutu ga daliban jihar.

Ma’aikatar ilimi ce ta sanar da haka a safiyar yau Litinin.
A wata sanarwa da mai Magana da yawun ma’aikatar Aliyu Yusif ya fitar ya ce gwamnatin ta ƙara mako guda a maimakon ranar da a ka sanya za a koma.

A halin yanzu za a koma makaranatu a jihar a ranar 12 ga watan Satumba maimakon ranar 5 ga watan Satumba da a ka saka a baya.

Matakin hakan ya zo domin daidaita zangon karatun da a ka samu cakuɗewar sa saboda hutun dole da a ka tafi a sakamakon annobar Korona.
Hukumar Ilimi a jihar ta ce an saka ranar Lahadi 12 ga watan Satumba da daliban makarantun kwana za su koma, yayin da ɗaliban makaranatun je ka dawo za su koma a ranar Litinin 13 ga watan Satumba.