Rundunar sojin Najeriya sun fatattaki yan bindiga daga maɓoyar su a dajin Sububu.

Dakarun sun kai hari ta sama ne sannan su ka kori yan bindigan da ke ɓoye a wata makaranata a cikin dajin.

Hare-haren da su ka kai  yankunan  Jjaaye da Dammaka kuma maɓoya ce ga manyan ƴan bindiga da ke kai hare-hare Zamfara.

Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewar dakarun sojin sun lalata makaman ƴan bindigan sannan su ka lalata dajin da su ke ɓoye a ciki.

Haka kuma an kashe ƴan bindiga sama da 50 a wani hari da sojoji su ka kai ƙauyen Gidan Rijiya sannan a ka lalata makaman su.

Guda cikin dakarun jami’an tsaron hadin gwiwa ya tabbatar d acewar sun yi nasara a kan dukkan hare-haren da su ka kai wa ƴan bindiga a ƙarshen makon da ya gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: