Buhari ya bayyana haka ne a cikin saƙon da ya aikewa al’umar Jos don su rungumi zaman lafiya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya roƙi al’umar jihar Plateau da su rungumi zaman lafiya tare da guzewa fitina da rikici.

Shugaban ya miƙa wannan roƙo ne a wata sanarwa da mai Magana da yawun sa Malam Garba Shehu ya fitar.

Ya ce a wannan lokaci gwamnatin na yin duk mai yuwuwa wajen ganin an kawar da duk wata hanyar da za ta haifar da tashin hankali a Najeriya.

Shugaba Buhari ya ce ya kamata mutane su dinga fuskantar irin ƙoƙarin da su ke yi don kawar da fitina a fadin ƙasar.

Haka kuma ya ce dole ne malamai da sarakuna da sauran shugabanni su tabbatar sun kaucewa duk wata hanya da ka iya haifar da rikici ko kuma rura wutar rikici.

Buhari ya ce akwai matsaloli masu yawa da ake fuskanta a ƙasar kuma ya kama mutanen ƙasar su dinga fuskantar irin ƙoƙarin da su ke yi don kaucewa fitina.

Leave a Reply

%d bloggers like this: