Rundunar yan sanda a Zamfara ta yi nasarar kubutar da mutane takwas da yan bindiga su ka sace a jihar.

Ƴan bindiga sun sace mutanen a Kangon Sabuwa da ke ƙaramar hukumar Bagudu ta jihar Zamfara a ranar 25 ga wtaan Agustan da mu ke ciki.
Ƴan sandan su ka ce sun kuɓutar da mutanen saga sansanin ƴan bindiga na Kungurmi ba tare da biyan ko sisin kwabo ba.

Kakakin yan sandan jihar SP Muhammad Shehu ya ce an duba lafiyar mutanen da a ka kuɓutar sannan a kan miƙa su ga iyalan su.

A sanarwar da kakakin ya fitar a yau Talata ya ce aikin jami’an ne tabbatar da cewar an tsare rayuka da lafiyar al’umma.
Sannan za su ci gaba da aiki da jami’an tsaro don tabbatar da ci gaba da aikin tsare lafiya da rayuwar al;umma.
Haka kuma ya jinjina wa jami’an tsaro da su ke aiki don tabbatar da zaman lafiya a jihar baki ɗaya.