Gwamnatin jihar Kaduna ta haramta cin kasuwar mako-mako a fadin ƙananan hukumomi biyar na jihar.

A wani salon a magance matsalar tsaro da a ke fuskanta a jihar, gwamnatin ta haramta siyar da mai a galan da kuma siyar da shi a bakin titi.

Kwamishinan harkokin tsaro da al’amuran cikin gida a jihar Samuel Aruwan ne ya bayyana haka, y ace an dauki matakin ne don magance matsalar tsaron da a ka dade a na fuskanta a jihar.

Dokar za ta yi aiki ne a ƙananan hukumomin Igabi, Birnin Gwari, Kajuru, Chikun da ƙaramar hukumar Giwa.

Sannn gwamnatin ta haramta wa gidajen mai siyar da mai a ckin jarka.

Jihohi uku kenan da su ka ɗauki salo iri daya a ƴan kwanakin nan don magance matsalar tsaron da ta ki ci ta ƙi cinyewa a cikin su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: