Gwamnatin jihar Katsina ta rufe wasu kasuwanni da tituna a jihar a wani salon a daƙile ayyukan ƴan bindiga a jihar.
Gwamnan jihar Aminu Bello Masari ne ya bayar da umarnin hakan a yau Talata tare da dakatar da cinikin dabbobi a wasu yankunan jihar.
Daga cikin titinan da a ka hana a dinga bi akwai babban titin Jibia zuwa Gurbin Ɓaure wanda a ka umarci matafiya da su sauya hanya zuwa Funtua.
Sannan an hana ababen hawa na haya bin titin Ƙanƙara zuwa Sheme shi kuma motocin gida kaɗai a ka amince su bi titin.
Sannan gwamnatin ta haramta wa manyan motoci shiga dazuka don dakko itace.
Haka kuma gwamnatin ta dakatar da cinikin dabbobi a Charanchi, Mai’adua, Safana, Faskari, Sabuwa, Ɓaure, Kaita, Kafur, Ƙanƙara, Duntsinma, Jibia, Batsari, Ɗanmusa da ƙaramar hukumar Malumfashi.
Sannan an haramta siyar da dabbobi tsakanin Katsina da sauran jihohi.
Haka kuma gwamnatin ta haramta ɗaukar mutane uku a babur mai ƙafa uku da a ka fi sani da adaidaita sahu, sannan an haramta cinikayyar babur na hannu a kasuwar Charanchi.
Haka kuma an haramta siyar da man fetur da yah aura dubu biyar sannan an hana siyar da shia cikin jarka.
Sannan a cikin Katsina an saka dokar hana hawa babur daga karfe shida na safe zuwa ƙarfe goma na dare, yayin da sauran ƙananan hukumomin jihar za a dinga hawa babur daga ƙarfe shida na safe zuwa karfe shida na yamma.
Wannan doka na zuwa ne bayan gwamnatin jihar Zamfara ta saka makamanciyar wannan doka a ƴan kwanakin nan.