Gwamnatin jihar Kano ta rufe wasu asibitoci masu zaman kan su a jihar.

Gwamnatin ta rufe asibitocin ne bayan samun su da gudanar da aiki ba tare da izini ko rijista ba.

A wata sanarwa da babban sakataren gudanarwa a hukumar asibitoci masu zaman kansu a Kano Dr. Usman Tijjani Aliyu ya fitar ya ce asibitocin na gudanar da aiki ba tare da lasisi ba.

An rufe asibitocin ne a ƙaramar hukumar Kumbotso a yayin da hukumar ke wani zagaye don ganin yadda ake gudanar da al’amuran lafiya a jihar Kano.

Sanarwar ta ƙara da cewa, bayan rufe asibitocin za a duba laifin da su ka aikata sannan a ɗauki matakin da ya dace a kan su.

Hukumar na yin wani zagaye don ganin yadda cibiyoyin lafiya ke gudanar da ayyukan su a fadin jihar Kano tare da tabbatar da cewar sun a bin matakan da su ka dace don tsare lafiyar jama’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: