Kotun shari’ar musulunci da ke ƙofar Kudu a Kano ta bayar da umarnin duba kwakwalwar sheik Abduljabbar Nasiru Kabara.
Hakan ya fito daga bakin alƙalin kotun Ibrahim Sarki Yola bayan Malamin ya gaza amsa tambaya ko guda daga cikin tuhumar da ake masa.
A yau Alhamis kotun ta sake zama don sauraron ƙarar da gwamnatin Kano ta shigar a kan malamin wanda ta ke zargin ya na yin ɓatanci ga fiyayyen halitta annabi Muhammad S.A.W tare da kalaman tunzira jama’a.
Lauyoyin malam Abduljabbar sun soki yadda kotu ke jan ƙafa a kan shari’ar sai dai alƙalin y ace tuhumar da ake masa wajibi ne sai an ji daga gare shi.
Alƙalin kotun ya gabatar da wasu tambayoyi ga malamin da ake tuhuma wanda ya gaza amsa ko da tambaya daya daga ciki.
An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 16 ga watan Satumban da muke ciki don ci gaba da sharia’ar.
Gwamnatin Kano ce ta yi ƙarar sheik Abduljabbar Kabara bayan ya buƙaci a shirya muƙabala, a yayin muƙabalar kuwa malamin y ace babu isashen lokacin da zai iya bayani a kan kalaman sa.