Gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da umarnin katse layukan sadarwa na wayar tarho a fadin jihar.

Hukumar sadarwa a Najeriya ta ce ta karɓi umarnin katse layukan wayar ne daga gwamnatin Zamfara a don haka ta ɗauki matakin haka.
Hakan na zuwa ne bayan ɗaukar wasu matakai da gwamnatin ke ganin hakan ne zai daƙile ayyukan ƴan bindiga da su ka addabi jihar.

Bayan ɗaukar sabbin matakai a kan tsaro ƴan bindiga su ka kai hari wata makaranta a Zamafara tare da sace ɗalibai da malamai dama da 70.

A wannan karon gwamnatocin jihohi na daukar salo iri ɗaya don ganin an daƙile ayyukan ƴan bindigan da su ka addabi yankunan arewa maso yammacin Najeriya.
Gwamnatin ta buƙaci hukumar sadarwa a Najeriya ta katse layukan sadarwa a jihar na wani lokaci don ganin an sami mafita a kan yaƙi da yan bindigan da ake yi.
A daidai lokacin da gwamnatocin jihohi ke ƙoƙarin sake salo a fannin tsrao su kuwa ƴan bindigan ke ci gaba da kai hare-hare a jihohin arewa maso yammacin Najeriya.