Ƙungiyar Miyetti Allah ta buƙaci masu ruwa da tsaki su shiga batun hana Fulani makiyaya kiwo a jihohin kudancin Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan majalisar dokokin jihar Enugu ta zartar da dokar hana kiwo a ƙasar.
Dokar da majalisar ta zartar wadda a ka yi bayan amincewar gwamnonin kudancin Najeriya su 17.

Gamayyar gwamnonin kudancin Najeriya sun amince da dokar hana Fulani makiyaya kiwo a yankiin su daga ranar ɗaya ga watan Satumban da mu ke ciki.

Dokar da majalisar dokokin jihar Enugu ta zartar ya sa hankalin Fulani ya tashi kamaryadda ƙungiyar ta bayyana.
Gamayyar gwamnonin kudancin Najeriya sun ɗauki wannan mataki ne don samar da tsaro a jihohin su.
Sai dai wasu ƴan Najeriya na ganin hakan a matsayin take damar da kundin tsarin mulkin ƙasa ya bayar da daman a wataya wa da kuma yin rayuwa a duk inda dan ƙasa ke buƙata.