Wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun sace wani dagaci a jihar Neja da ke Arewacin Najeriya.

An sace dagacin ne a fadar sa ranar Asabar da misalin ƙarfe tara na dare.

Dagacin  na garin Wawa da ke ƙaramar hukumar Borgu ta jihar

Wani a garin ya tabbatar da cewar mutanen da su ka sace basaraken sun je fadar ne sanye da kayan sojoji sannan su ka tafi da shi.

Ya ƙara da cewa mutanen kusan su goma su na ɗauke da makamai a hannun su sannan sun je ne a kan babubra..

Ƴan bindigan sun tafi da basaraken ne shi kaɗai ba tare da ɗaukar wani mutumi a garin ko fadar ba.

Har zuwa lokacin tattauna wa da mutumin ƴan bindigan bas u tuntuɓi iyalan basaraken a dangane da buƙatar su ba.

Jihar Neja na daga cikin jihohin da ke fuskantar ƙalubalen ƴan bindiga a arewacin Najeriya.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: