Gwamnatin jihar Kaduna da gwamnatin jihar Plateau sun ɗauki damarar aiki da sauran jami’an tsaro don magance matsalolin da su ka addabi jihohin biyu.

Gwamnonin biyu sun ƙulla wannan yarjejeniyar aiki ne yayin da gwamnan Kaduna Mlaam Nasir El’rufa’I ya kai wa gwamnan Plateau Simon Lalong ziyara a ranar Lahadi.
Gwamnan Kaduna ya kai ziyarar ne don jajanta wa a bisa kashe-kashen mutane da a ka yi a wasu yankunan jihar.

Gwamnan El’rufa’I ya ce jihohin Kaduna da Plateau ba maƙoftaka kadai su ka had aba sun haɗa alaƙar aiki mai ƙarfi don ganin an samar da zaman lafiya.

Ya ƙara da cewa a ƙoƙarin sun a ganin an samar da zaman lafiya a jihohin gwamnonin su ka I ƙoƙarin samar da hukumomi musamman a kan zaman lafiya.
A nasa jawabin gwamna Plateau Simon Lalong wanda mataimakin sa Farfesa Sonni Tyoden ya wakilce shi ya ce a tsawon lokaci jihar Kaduna da Plateau na da kyakkyawar alaƙa a don haka duk abin da ya shafi Plateau ya shafi Kaduna.
Gwamnan ya yaba wa El’rufa’I a bisa hadin kai wajen aiki da kuma nuna damuwa a kana bin da ya faru a kwanan nan.