Aƙalla mutane 18 ƴan bindiga su ka yi awon gaba da su a grin Keke na karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun shiga garin da misalign ƙarfe 12 na daren Litin wayewar Talata.
Wani da abin ya faru a kan idon say a shaida cewar, ƴan bindigan sun shiga garin da yawa ɗauke da makamai sannan su ka sace mutane 18 a ciki.

A daidai lokacin da ake ci gaba da ɗaukar matakai don ganin an kawar da ƴan bindiga a wasu daga cikin jihohin Najeriya ciki har da jihar Kaduna.

Daga cikin matakan da su ke ɗauka har da hana cin kasuwannin mako-mako wanda jihohi hudu na arewa su ka dauka da ciyar da mai a cikin jarka.
Har loikacin da mu ke kammala wannan labari ba mu samu ji daga ɓangaren jami’an tsaro a kan harin ba.
Gwamnan Kaduna Malam Nasir El’rufa’I ya sha alwashin daƙile ayyukan ƴan bindiga a jihar ba datare da ya yi sulhu da su ba.