Hukumar lura da yanayi a Najeriya ta sanar da wasu jihohi da ka iya fuskantar barazanar iska mai ƙarfi a Najeriya.

Shugaban hukumar Farfesa Mansur Baƙo ne ya sanar da hakan ya na mai cewa yanayin ya kai maƙura wajen yuwuwar sa.

Farfesa Baƙo ya ƙara da cewa jihohin Kano Katsina Zamfara da Kaduna da Kebbi na daga cikin jihohin da ka iya fuskantar hakan.

Ya ƙara da cewa sauran jihohin su ne Taraba Filato, Sokoto, Enugu, Legas da jihar Bauchi.

Daga cikin jihohin da ya lissafa y ace akwai wurin da ka iya fuskantar ambaliyar ruwan sama sai jihohin da za su iya fuskantar iska mai ƙarfi da kuma wurin da za su iya samun iska mai ƙarfi da kuma ambaliyar ruwan sama.

Yanayin na iya yuwuwa a ranakun Talata, Laraba, da kuma Alhamis.

Farfesa Baƙo y ace ba iya Najeriya ne kaɗai za su iya fuskantar haka ba hatta wasu daga cikin ƙasashen Afrika na iya fuskantar yanayin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: