PIC. 11. FULANI'S HERDSMAN CARRYING A CALF DURING THEIR MIGRATION ALONG WUNDI/RISHI TORO LOCAL GOVERNMENT AREA OF BAUCHI STATE ON THURSDAY (29/12/11).

Majalisar dokokin jihar Legas ta amince da dokar hana kiwo a jihar.

Hakan ya biyo bayan matsayar da gwamnatocin kudancin Najeriya su ka cimma a baya don ganin an hana makiyaya kiwo a jihohin su.

Majalisar ta amince da dokar haka kiwo a jihar a yau Alhamis bayan ta samu goyon bayan mafi rinjiyaye daga wakilai a majalisar.

An zartar da dokar bayan an tsallake karatu na uku ba tare da samun cikas daga mambobin majalisar ba.

Majalisar ta saurari ra’ayin al’umar jihar a dangane da dokar ranar Laraba.

Shugaban majalisar ya gode wa wakilai a majalisar a bisa hadin kai da ya samu wajne kafa tarihi a jihar.

Gwamnonin kudu a Najeriya sun lashi takobin hana kiwo a yankunan su tun bayan da aka fara samun masu garkuwa da mutane.

Jihar Enugu ce ta fara yanke hukuncin tare da zartar da dokar hana makiyaya kiwo a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: