Shugaban Ya yi wannan furuci ne yayin da ya kai ziyarar aiki jihar Imo a yau Alhamis.

Shugaban Njaeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar da bayar da goyon bayan yaƙi da masu tayar da ƙayar baya na jihar Imo.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yayin da ya kai ziyarar aiki jihar a yau don ƙaddamar da wasu aikace-aikace a jihar.

Ya ce gwamnatin sa za ta taya jihar imo wajen yaƙi da yan bindiga da sauran masu aikata muggan laifuka a jihar.

Shugaban ya ce babu wata al’uma da za ta ci gaba muddin a na fuskantar matsalar tsaro.

Buhari ya lashi takobin kawo karshen tashe-tashen hankulan da a ke fuskanta a jihar.

Jihar Imo cibiya ce da ƙungiyar IPOB ke da ƙarfi daga cikin jihohin da ke iƙirarin ɓalle wa daga Najeriya tare da kafa ƙasar BIAFRA.

Leave a Reply

%d bloggers like this: