Ƴan bindigan sun karɓi shinkafar sannan su ka saki wata yarinya a jihar.

Ƴan bindiga a jihar Sokoto sun fara karɓar kayan abinci a maimakon kudin fansa daga al’uma.
Wani mazaunin ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar ya shaida cewar an saki yarinyar maƙofcin sa bayan an kai wa ƴan bindigan kayan abinci.

Ya ce kwanon shinkafa goma a ka kai wa ƴan bindiga sannan su ka saki yarinyyar.

Sannan ƴan bindigan sun buƙaci a basu buhun shinkafa da kwalayen taliya a don fansarw ani direba da su ka kama.
A baya sun buƙaci a basu kudi naira miliyan 15 kafin sakin direban sai dai a yanzu sun sauya shawara daga karbar kudin zuwa buhun shinkafa da kwalayen taliya.
Wannan al’amari na zuwa ne bayan gwamnatocin jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna, Neja, da Sokoto sun ɗauki matakin hana cin kasuwannin mako-mako a jihohin su.
Matakin da gwamnatocin su ka dauka don maganace ta’addancin ƴan bindiga a jihohin su.