Rundunar ƴan sandan jihar Neja ta yi nasarar kubutar da hakimin da ƴan bindiga su ka sace a jihar Neja.

An kuɓutar da hakimin a ranar Juma’a bayan da yamma.

Kakakin yan sandan jihar Wasiu Abiodun ne ya sanar da haka a ranar Asabar.

Ya ce jami’an ƴan sanda sun kubutar da hakimin haɗin gwiwa da rundunar soji da kuma ƴan banga.

An sace hakimin ne a fadar sa ranar Asabar da daddare.

Hakimin ya shafe kwanaki shida ya shafe a hannun ƴan bindiga.

Leave a Reply

%d bloggers like this: