Ƙasa da mako guda da shugaban ya buƙaci su janye yajin aiki tare da koma wa bakin aikin su.

Ƙungiyar likitoci masu neman kwatrewa a Najeriya sun ƙi aminta da kiran shugaba Buhari don janye yajin aikin da su ke ciki.
A wani saƙon martini da su ka mayar bayan shugaban ya buƙaci su janye yajin aikin, ƙungiyar ta ce hanya mafi sauƙi da za su iya karɓa don janye yajin aikin shi ne biyan su haƙƙoƙin da su ke bi tun daga shekarar 2014 zuwa shekarar 2021.

Su k ace ya kamata shugaban ya bayar da umarnin biyan su haƙƙoƙin su maimakon roƙon su da su janye yajin aikin.

Sai dai ministan a Najeriya y ace likitocin na bin bashin albashin wata guda ne kacal.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana wa likitocin cewar za a biya su dukkan haƙƙoƙin da su ke bi bayan an kammala tantancewa.
Ƙungiyar ta zayyano wasu dalilai na ƙin koma wa bakin aikin su, ciki har da kokawa a kan rashin kudin da za su yi sufuri zuwa wajen aikin da kudin da za su biya wa ɗaliban su kudin makaranta.
Ƙungiyar ta tsunduma yajin aiki ne bayan ƙin mutunta yarjejeniyar da su ka ce ɓangaren gwamnati ta ƙi yi musu bayan kwanaki 100 da alƙawarta cewar za su biya su haƙƙoƙin su.