Wasu da ake zargi ƴan ƙungiyar IPOB ne sun kai hari wata makaranatar sakandire a jihar Imo.

Hakan na zuwa ne ƙasa da mako guda da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki jihar tare da alƙawarin magance matsalar tsaro.
Maharan sun kai harin a safiyar yau yayin da ɗaliban ke ƙoƙarin ubuta jarrabawa a makarantar.

Ƴan bindigan sun fara harbin iska al’amarin da ya sanya ɗaliban da malamai su ka tarwatse.

Ƴan bindigan sun ƙone wasu ababen hawa mallakin ɗalibai da malaman makarantar.
Jihar Imo cibiya ce ta ƙungiyar IPOB mutanen da ke iƙirarin balle wa daga Najeriya tare da kafa ƙasar BIAFRA.