Ƴan kasuwar Kano sun yi murnar samar da kasuwar dalar gyaɗa wadda aake kan gina wa a halin yanzu.

Sun ce samar da kasuwar zai taimaka wajen bunkasa kaauwanci a Kano.

Hakan ya faru ne yayin da aka yi wani taron bunkasa kasuwanci a Kano.

Kamfanin MN ATAJ CONSTRUCTION LIMITED AND A VENTURES INDUSTRIES ne su ke samar da shaguna sannan su siyar ga jama’ar da ke bukata.

Taron da aka yi a Kano domin farfaɗo da kasuwancin a ranar Lahadi.

Manyan ƴan kasuwa ne su ka samu damar halartar taron,

Daga ciki akwai Alhaji Sabi’u Ahmad Maiturare, Alhaji Bature Abdulaziz, Alhaji Sabi’u Baƙo sai Alhaji Bashir Othman Tofa.

Injiniya Rabiu Sufi wanda ya wakilci ya yi godiya tare da fatan kasuwar ta zama sila ta ƙara haɓakar kasuwanci a Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: