Wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun kashe wani jami’in soja sannan su ka sace wata mata da ɗan ta a Zaria.

Ƴan bindigan sun shiga unguwar Milgoma sannan su ka fara harbin iska wanda hakan ya basu damar tafiya da matar.
Kusan su 30 su ka shiga unguwar ɗauke da muggan makamai da misalin ƙarfe tara na daren jiya Litinin.

Yayin da su ka shiga unguwar mutanen unguwar sun yi ƙoƙarin sanar da jami’an tsaro al’amarin da yayi sanadiyyar rasa ran wani soja yayin musayar wuta.

Har lokacin da muke kammala wannan labari babu tabbacin hakan daga ɓangaren jami’an tsaro.
Idan ba a manta ba ƴan bindiga sun sace ɗalibai a Zaria tare da sace wasu mutane a garin.
Jihar Kaduna na daga cikin jihohin da ƴan bindiga su ka fi addaba a arewa maso yammacin Najeriya.