Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Akwai Yuwuwar Mazauna Gidan Yari Su Yi Zaɓe A Shekarar 2023

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara yin duba a kan matakin da za ta bi don ganin an bai wa ɗaurarru mazauna gidan yari damar yin zaɓe.

Sakatare a hukumar al’amuran cikin gida a Najeriya Dr. Shu’aib Belgore ne ya tabbatar da haka a yayin da wata kungiya ta ziyarce shi a Abuja.

Ya ce duba ga zaɓen 2023 da yake tikaro wa hukumar na duba hanyoyin da su ka cancamta don ganin an bai wa mazauna gidan yari damar kaɗa ƙuri’a.

Dr. Shu’aib ya ce akwai abin duba wa ganin yadda ake kai hare-hare gidan yari har ma ya bayar da misalin harin da aka kai jihar Kogi a ranar Lahadi.

Kuma a dailin haka gwamnatin na damuwa ganin hakan ya haifar da cikar kuma za su sake tunani don ganin an bayar da kariya ga mazauna gidajen yari.

Ya ce idan lokaci ya yi za su duba hanyoyin da za a bi doon ganin an bayar da cikakkiyar kariya ga mazauna gidan yari a yayin zaɓen.

Aikin bayar da damar zaɓen y ace sun a kan duba dukkanin hanyoyin da su ka dace don ganin an samar da wurin zaɓe, da wurin karbar katin zaɓen yadda za a gudanar da shi cikin tsari.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: