Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Bayar Da Umarnin Tuɓe Shugaban Hukumar Tattara Haraji

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da tsige shugaban hukumar tattara haraji ta jihar.

A yau Talata majalisar ta buƙaci gwamnatin Kano da ta gaggauta cire Abdurrazaƙ Salihi daga muƙamin shugabancin hukumar.

A ranar Litinin majalisar ta yis ammacin shugaban hukumar don ytin bayani a dangane da koma bayan da jihar Kano ta samu a ɓangaren tattara haraji duk da cewar ita ce cibiyar kasuwanci.

Kano ita ta kasance ta 10 cikin jerin jihohin da su ka samar da haraji mai yawa, kuma hakan koma baya ne sosai la’akari da shekarun baya.

Shugaban majalisar Hamisu Chidari ya ce ɗabi’ar shugaban hukumar ce ta sanya su ka ɗauki matakin hakan.

Shugaban ya ƙi gabatar da tsarin haraji9n da aka karɓa wanda majalisar ta buƙaci ya yi.

Ko a  ɓangaren gwamnatin ta zargi shugaban da yanke hukunci rage wani ɓangare na haraji wanda hakan ya saɓa da kundin tsarin mulki.

Tuni majalisar ta yi kwamitin mutane takwas da za su yi bincike a kan badaƙalar da ake zargi shugaban hukumar tattara haraji ya yi.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: