Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Tilas Ce Ta Sa Za Mu Sake Ciyo Bashi Don Yiwa Al’umma Aiki – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce dole ce ta sa ya sake ciwo bashi don aiwatar da ayyukan da za su amfani al’umma.

Shugaban ya bayyana haka ne a wata wasiƙa da ya aike wa majalisar dattawan ƙasar kuma yake buƙatar su sahale masa don sake ranto kudin da ya haura tiriliyan ɗaya da rabi.

A ƙunshin wasiƙan da shugaban ya aike wa majalisar, shugaban ya buƙaci a bashi damar sake ciyo bashin kudi naira triliyan ɗaya da biliyan ɗari shida da sittin da takwas da miliyan ɗari hudu da goma sha bakwai,da dubu ɗari biyu da ashirin da tara da ɗari da ashirin da huɗu da ɗigo biyar.

Shugaban majalisar ya ce an tsara karbar bashin tun a shekara 2018 zuwa shekarar 2020.

Za a ciyo bashin ne daga bankin duniya da wasu bankuna da ƙungiyoyi.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: