Rundunar sojin samar Najeriya ta yi luguden wuta a kan fararen hula a jihar Yobe.

Al’amarin ya faru a ranar Laraba a garin Buhari da ke ƙaramar hukumar Yunusari ta jihar Yobe.
Jirgin ya yi luguden wuta a kan mutanen ƙauyen sannan ya kashe wasu da dama.

Rundunar sojin saman ta musanta kai harin a kan mutanen sai dai daga baya kuma ta ɗauki alhakin kai harin wanda ta ce ta yi ne bisa kuskure.

A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin Edward Gabkwet ya fitar, ya ce jirgin yaƙin su ne ya yi kuskuren yin luguden wuta a kan ƴan ba ruwa na a garin.
Rundunar sojin na aika jiragen yaki don yaƙar ƴan ta’addan da su ka addabi ƙasar a arewacin Najeriya.
Ko a baya sai da wani jirgi ya taɓa yin luguden wuta a kan dakarun sojin ƙasan Najeriya.
A wancen lokacin ma sun bayar da sanarwar hakan ya faru ne cikin kuskure.