Sakataren riko a jam’iyyar APC John Akpanudeodehe ya ce a shirye jam’iyyar ta ke don bai wa tsohon shugaban takara a shekara ta 2023.

Sakataren ya bayyana haka ne a cikin wata hira da ya yi da gidan talabiji na Channels.
Ya ce abin alfahari ne a gare su idan ya zamto tsohon shugaban ƙasar ya kjoma cikin jam’iyyar.

sannan jam’iyyar a shirye ta ke da ta ba shi takarar shugabancin ƙasar a shekarar 2023.

Tsohon shugaban wanda ya mulki ƙasar tsawon shekaru shida ya sha kayi a shekarar 2015.
Jam’iyyar APC ta doke Jam’iyyar PDP a shekarar 2015 yayin da guguwar sauyi ta zo wanda hakan ya bai wa mutane da dama na jam’iyyar APC damar ɗare wa kan madafun iko.
Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ya sha su ka a kan yadda ake gani taɓarɓarewa tsaro ta ta’azzara a zamanin mulkin sa.
Mayan Boko Haram sun sha kai hare-hare a zamanin sa wanda jami’iyyar APC ta sha alwashin magance matsalar staron da zarar ta samu damar mulkar ƙasar.