Connect with us

Labarai

Yara Miliyan Guda Na Iya Ƙauracewa Makarantu A Najeriya – UNICEF

Published

on

Hukumar kula da ƙananan yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF ya ce a Najeriya an yi garkuwa da ɗalibai dama da dubu ɗaya.

A wani rahoto da hukumar ta tattara a kan yadda ƴan ta’adda ke kai hare-hare makarantu tare da sace ɗalibai.

Hukumar ta ce akwia yuwuwar fargabar sace ɗaliban ya yi sanadiyyar raba yara miliyan ɗaya daga makarantu.

Daga cikin makarantun da hukumar ta tattara alkaluman tare da fitar da hasashen akwia makarantun firamare da sakandire da kuma ɗaliban jami’a.

Hukumar ta ce fargabar rashin tsaro ce za ta yi silar raba mutanen daga makarantn.

Akwai ɗalibai da dama da ke hannun yan bindiga waɗanda aka sace daga makarantu daban-daban na jihohin ƙasar musamman ma arewaci.

Satar ɗalibai tare da neman kuɗin fansa wani saloo ne da yan bindigan su ka ɗauka daga baya, bayan ɗauki ɗaiɗai da su ke yi wa mutane a cikin gari ko kan tituna.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Yan Sanda A Osun Sun Kama Mutumin Da Ya Kashe Mahaifiyarsa

Published

on

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Osun sun kama wani mutum mai suna Lukman Adejoju bisa zargin kashe mahaifiyarsa dattijuwa mai suna Aminat.

 

Jaridar Punch ta ruwaito a ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilu cewa Lukman, mazaunin kauyen Kajola ne da ke kusa da Apomu a jihar Osun.

 

Rahoton ya bayyana cewa mutumin ya kashe mahaifiyarsa, wadda aka ce tana da shekaru kusan 100 a duniya, sakamakon takaddamar da ta shiga tsakaninsu kan manja.

 

Wani ganau mai suna Rasaki ya bayyana a ranar Lahadi cewa Lukman da mamaciyar sun dauki wani lebura ne wanda ya taimaka musu wajen siyar da wasu jarakunan manja.

 

Yayin da leburan ya dawo masu da kudin, an ruwaito marigayiya Aminat ta dage cewa sai dai a ba ta kudin, lamarin da ya harzuka dan nata Lukman.

 

 

 

 

Continue Reading

Labarai

DSS Sun Kama Ta Hannun Damar Nasir El-Rufai

Published

on

Jami’an hukumar DSS sun kama wata ƴar siyasa ta jam’iyyar APC, Aisha Galadima, a jihar Kaduna.

 

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kama ƴar siyasar wacce ta hannun daman tsohon gwamnan jihar, Nasir Ahmad El-Rufai ce a ranar Lahadi, 14 ga watan Afirilun 2024.

 

Rahoton ya nuna cewa kamun da aka yi mata na da nasaba da wani rubutu da ta yi a soshiyal midiya kan gwamnan jihar Malam Uba Sani.

 

A cewar majiyoyi, Aisha Galadima ta caccaki Gwamna Uba Sani bisa kalaman da ya yi kan Nasir El-Rufai, a shafinta na Facebook.

 

Wani maƙwabcinta ya bayyana cewa an kamata ne a gidanta da ke unguwar Tudun Wada a Kaduna a ranar Lahadi, yayin da wata ƙawarta ta ce an kashe wayoyinta bayan kamun da aka yi mata.

 

Sai dai, babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan Kaduna, Muhammad Lawal Shehu, ya ce bai da masaniya kan kamun da aka yi mata.

 

Shehu ya yi nuni da cewa a tuntuɓi hukumar tsaron farin kaya ta DSS domin samun ƙarin bayani kan lamarin.

Kuma har kawo wannan lokaci, hukumar ba ta ce komai dangane da kamun da ta yi wa matar ba.

 

 

 

 

Continue Reading

Labarai

EFCC Ta Kwato Biliyan 32.7 Da Aka Wuwure A Ma’aikatar Jin-kai

Published

on

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa a Najeriya EFCC ta ce ta ƙwato Naira biliyan 32.7 da $445,000 da ake zargin wawushe a ma’aikatar jin ƙai da yaƙi da fatara.

 

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa a shafin X da kakakinta, Dele Oyewale, ya fitar a ranar Lahadi, 14 ga watan Afirilun 2024.

 

EFCC ta bayyana hakan ne bayan abin da ta kira yadda ake ta yawan maganganu kan binciken da take yi a ma’aikatar jin ƙai da yaƙi da fatara.

 

Oyewale ya yi bayanin cewa a farkon binciken da hukumar ta fara, ta gayyato tsofaffi da dakatattun jami’an ma’aikatar domin jin daga bakinsu.

 

A cewar kakakin na EFCC, hukumar ta kuma fara binciken wasu ayyukan zamba da suka haɗa bashin da aka ciyo daga bankin duniya, kuɗaɗen Covid-19 da kuɗaɗen da aka karɓo na Abacha waɗanda aka ba ma’aikatar domin rage raɗaɗin talauci.

 

A farkon fara bincike, an gayyato tsofaffi da dakatattun jami’an ma’aikatar jinƙai, kuma binciken da ake yi kan zargin zamba ya sanya ya zuwa yanzu an ƙwato N32.7bn da $445,000.

 

Binciken kuma ya bankaɗo jami’an ma’aikatar masu yawa waɗanda ake zargin da hannunsu wajen yin sama da faɗi da kuɗaɗen.

 

Rundunar yan sandan a jihar Osun sun kama wani maidanci bisa laifin kashe mahaifiyarsa.

 

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: