Rundunar ƴan sanda a Sokoto ta tabbatar da mutuwar mutum guda tare da sace wasu mutane a garin Tangaza da ke karamar hukumar Tagaza ta jihar.

Mi magana da yawun yan sandan jihar ASP Sunusi Abubakar ne ya bayyana haka a yau Asabar yayin zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN.

Ya ce al’amarin ya faru a yammacin Juma’a yayin da yan bindiga su ka kewaye garin sannan su ka tafi da wasu da ba a kai ga gano adadin su ba.

A sakamakon harin akwai wasu da su ka samu rauni sannan an kai su asibiti don kula da lafiyar su.

Kakakin yan sandan jihar ya tabbatar d acewar sun hada kai da sauran jami’an tsaro don ganin an ceto mutanen da yan bindigan su ka sace.

A na zargin ƴan bindiga na shiga maƙotan jihohin Zamfara bayan rufe layukan sadarwa da kuma hana cin kasuwannin mako-mako.

Leave a Reply

%d bloggers like this: