Shugaban Najeriya Muhamamdu Buhari zai tafi Amurka don halartar babban taron majalisar dinkin duniya UNGA karo na 76.
Taron da aka buɗe a ranar 14 ga watan Satumban da mu ke ciki, kuma a na sa ran shugaban zai yi jawabin sa a ranar Juma’a makon da za mu shiga.
Babban taron da aka fara a birinin NewYork wada ake tattauna wa a kan batun farfaɗowa daga annobar Korona da kuma hanyar da za a bi don ɗorewar cigaba.
Shugaban ya tafi ƙasar da wasu muƙarraban sa ciki har da mai bashi shawara a kan harkokin tsaro.
Sannan zai kebe da wasu shugabannin ƙasashe bayan kammala taron.
Sanarwar da mai magana da yawun sa Femi Adesina ya fitar ya ce a na sa ran shugaban zai tafi gobe Lahadi sannan zai dawo a ranar Lahadi bayan kammala taron.