Rundunar ƴan sandan jihar Ogun ta ja hankalin al’umar jihar da su ƙauracewa taron addu’o’i musamman a yankunan da su ke kusa da daji.

Hukumar ta buƙaci mutane da su dakatar da hakan ganin yadda ƴan bindiga ke amfani da damar wajen sace mutane a garin.
Mai magana da yawun yan sandan jihar Abimbola Oyeyemi ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Ya ce hukumar ta fahimci akwai wasu mutane da su ke da ɗalibi’ar shirya taron addu’a a unguwannin da su ke kusa da daji kuma hakan babbar barazana ce ga lafiya da rayuwar su.

Ya ƙara da cewa hukumar ba ta yi hakan ne don take haƙƙin ƴan jihar wajen gudanar da addini ba illa tsare lafiya da rayuwar su.
Sannan hukumar ta ƙara jan hankalin mutane da su ci gaba da kaucewa duk wata hanya da za ta bai wa yan bindiga da,mar sace mutane ko yin barazana a gare su.