Gwamnatin jihar Katsina ta ce an kubutar da wasu mutane 20 waɗanda yan bindiga su ka sace a watanni biyar da su ka gabata.

Sai dai gwamnatin ta ce ta karɓi mutanen dauke da jariri sabuwar jhaihuwa,

Sakataren gwamnatin jihar Katsina ne ya bayyana haka bayan ya karɓi mutanen waɗanda daga ciki akwai yan ƙasa da shekaru 10

Sakataren ya ce mutanen sun kuɓuta ne yayin da ƴn bindiga su ka firgita a maɓoyar su bayan wani jirgin sojin saman Najeriya ya yi shawagi a yankin.

Tuni gwamnatin ta bayar da yumarnin duba lafiyar su a matsakin farko kafin wani tallafi da za ta yi musu wanda zai zo daga baya.

Wata mai sun Sahura Haruna ta ce ta haihu ne a waje da yan bindigan su ka killace su a cikin daji.

Sama da watanni biyar su ke hannun yan b indigan tun bayan da su ka sace su.

Gwamnatin ta ce za ta mayar da su ga iyalan su da zarar ta tabbatar da lafiyar kowanne daga cikin su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: