Shugaban mabiya mazahabar shi’a a Najeriya Ibrahim Zakzaky ya gana da mabiyan sa waɗanda su ka yi artabu da jami’an tsaro a shekarar 2015.

Shugaban ya gana da su tare da jajajanta musu da yi musu ta’aziyyar mutanen da su ka rasa rayuwarsu a ranar.

Sheik Ibrahim Zakzaky ya gana da mabiyan sa tare da matar sa Malama Zinat.

Malamin ya gayyaci iyalan mutane tare zuwa masaukin sa don jajanta musu kuma ya nemi afuwar hakan a maimakon zuwa ƙafa da ƙafa har inda su ke.

Sannan ya ja hankalin mabiyan sa da su kasance masu juriya da jajircewa a kan gaskiya.

Kotu ta sallam i Sheik Zakzaky da matar sa Malam Zinat bayan ta wanke su daga zargin da ake yi a kan su.

Sai dai gwamnatin jihar Kaduna ta ce za ta daukaka ƙara a kan zargin da ta ke masa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: