Rundunar yan sanda a Katsina sun kama wasu mutane da ake zargi su na kai wa ƴan ta’adda man fetur da kayan abinci.

A wata sanarwa da kakakin yan sandan jihar ya fitar a ranar Litinin y ace ƴan sanda sun kama mutane biyar kuma guda hudu daga cikin su su na kai wa ƴan bindiga man fetur shi kuwa ɗayan na kai musu biredi.

Daga cikin waɗanda a ka kama akwai wani mai shekaru 32 a duniya da ya ɗakko man fetur tun daga maradin jamhuriyar Nijar zuwa dajin Katsina don kai wa ƴan bindiga.

An kama mutumin ne a ranar 18 ga watan Satumban da mu ke ciki.

Kakakin yan sandan jihar Isah Gambo ya shaida cewar sauran mutane hudu da su ka kama ƴan jihar Katsina ne kuma a wurare daban-daban.

An kama mutanen a yayin dasu ka ɗakko ma fetur ɗin kuma su ke ƙoƙarin shiga daji don kai wa ƴan bindigan.

Tuni su ka ci gaba da gudanar da bincike a kan su kuma za su dauki matakin doka a gaba da zarar sun kammala bicike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: